IQNA

Amfani Da Fasahar Gyaran Tsoffin Littafai Ta Qom A Algeria

23:45 - November 01, 2016
Lambar Labari: 3480898
Bangaren kasa da kasa, Firayi ministan kasar Algeria a yayin halartar taron baje kolin littafai na kasar ya bayyana cewa za a yi amfani da fasahar adana littafai ta Qom a kasar Algeria.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na qom news ya habarta cewa, Abdulmalik Salal firayi ministan kasar Algeria da kuma firayi ministan kasar Nijar sun halarci taron bude babban baje kolin littafai na kasar Algeria wanda aka saba gudanarwa a kowace shekara.

A lokacin da suke ran gadi sun ziyarci rumfar baje kolin littafan kasar Iran, inda firayi ministan na kasar Algeriya yay aba matuka da irin fasahar da ka yi amfani da ita wajen adana dadaddun littafai a birnin Qom, inda tabbas za su yi amfani da irin wannan fasaha wajen adaa litatfan addini kasarsu.

Sala ya ce zai halarci taron bude babban baje kolin littafai na duniya a birnin Tehran wanda za a gudanar a cikin wata mai kamawa.

An bayar da kyautar wasu litatfai wadanda aka rubuta akasar ta Iran kyuata ga firayi ministan Algeria, daga ciki kuwa har da littafin sanin Iran, da kuma litatfai na tarihi da na adabi da aka rajama a cikin harshen larabaci.

Madaba’antu 671 ne na kasashen ketare suke halartar wannan bae koli, sai kuma marubuta adabi 60, da kuma cibiyoyin buga litatfai na cikin gida 900, da kuma littafai da adadinsu ya kai dubu 30 da aka baje kolinsu a wurin.

3542306

captcha