IQNA

Kamfe Mai Take A Tseratar Da Makarantan Kur’ani A Sudan

23:28 - October 16, 2017
Lambar Labari: 3482006
Bangaren kasa da kasa, wasu masu fafutuka a kasar Sudan sun fito da wani sabon kamfe mai taken a tseratar da daliban makarantun ku’ani na gargajiya a Sudan.
Kamfe Mai Take A Tseratar Da Makarantan Kur’ani A SudanKamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, jaridar AlqudsAlarabi ta bayar da rahoton cewa, bisa ga al’ada a kasar Sudan ana koyar da karatun kur’ani ta hanyar gargajiya, ko kuma makarantun allo.

A cikin wadannan lokuta an samu wasu masu fafutuka a kasar Sudan sun fito da wani sabon kamfe mai taken a tseratar da daliban makarantun ku’ani na gargajiya ko makarantun allo a kasar, sakamakon yadda malaman irin wadannan makarantu suke azabtar da almajiransu.

Masu fafutukar suka ce ana samun wasu malaman wadanda sukan sanya almajirai a cikin kunci da takura domin tilasta su yi karatun kur’ani ko harda, ta hanyar saka musu mari a kafafunsu.

Wani faifan bidiyo da aka nuna na wani yaro da ke karatun kur’ani a wata makaranta a jahar Nilu ta gabas, ya dauki hankulan kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasar da ma na kasashen ketare, inda aka nuna yaron daure da mari, yana cikin damuwa da rashin natsuwa da bain ciki.

A lokacin da aka tambaye dalilin da yasa ak sanya masa mari sai y ace, kawunsa ne ya kawo wurin malamin ya ce a saka ms mari domin ya zauna makaranta ya yi karatu.

Masu kare hakkin ‘yan ada Sudan sun e dole ne a kawo karshen irin wannan salon a kuntata ma almajirai da sunan ana koyar da su kur’ani.

3653228

captcha