IQNA

Bayanin Ayoyin Kur’ani Ta Hanya Mai Sauki

22:48 - October 18, 2017
Lambar Labari: 3482011
Bangaren kasa da kasa, tafsiril wajiz wani littafin tafsiri ne da Allamah Musatafa bin Hamza dan kasar Morocco ya rubuta wanda a cikinsa ya yi bayani kan ayoyin kur’ani ta hanya mai sauki.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani ya habarta cewa, shafin yanar gizo na oujdacity.net cewa, Mustafa bin Hamza mai bincke matuka kan ilmomin kur’ani, ya rubuta littafin tafsiri wanda ya kira da alwajizfi tafsiril kur’an wanda aka rubuta a cikin shafuka 423.

A cikin wannan tafsiri an bayyana lamurra da suka shafi tarihi da yanayin rayuwar mutane da abubuwan da suka hada rayuwar al’ummomi da kuma abubuwan da suka raba su ta fuskoki daban-daban.

Marubucin yay i kokari wajen ganin ya isar da sakon kur’ani ta hanya mai sauki, ba tare da yin amfani da salon a kalmomin ilimi, yakan yi amfani da salo mai sauki wanda kowa zai iya karantawa kuma ya fahimta tare da ilmantuwa.

Baya ga lamurra da suka shafi rayuwar al’ummomi ta zamantakewa da kuma tarihi da kyawan darssa na kur’ani da ke koyar da dabiu na gari, marubucin kuma ya mayar da haknali kan lamurra da suka shafi hukunce-hukunce da suka zo a cikin kur’ani.

Akwai surorin da ya yi amfani da harshen a ilimi wajen bayani a cikin su, kamar surorin Ra’ad, Ibrahim, Hijr, Nahl, Isra’i da kuma kahf, inda ya bayyana wasu lamurra da suke bukatar bayani na ilimi.

3654136


captcha