Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Prof. Klaus von Stosch ya samu babbar kyauta ta Jamhuriyar musulunci ta Iran ta shekara ta 2018, wadda shugaba Rauhani da kansa ya mika masa.
Shugaban kasar ta Iran ya bayyana wannan littafi da cewa shi ne littafin da ya fi dacewa da kyauta a wannan shekara, domin kuwa ya bayyana matsayin kur’ani mai tsarki kan yadda yake kallon sauran addinai da aka saukar daga sama, musamman ma addinin kiristanci, inda ya tabbatar da cewa musulmi da kiristoci ba makiyan juna ba ne.
Haka nan kuma littafin yana kara karfafa zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin bangarorin biyu, ta hanyar tabbatar da hakan daga abin da kur’ani mai tsarki ya fada.