IQNA

Kasashen Duniya Na Ci Gaba Da Yin Allawadai Da Bude Ofishin Jakadancin Amurka A Quds

23:49 - May 14, 2018
Lambar Labari: 3482657
Bangaren kasa da kasa, kasashen duniya da dama da suka hada da Iran, Rasha, Turkiya, Morocco, Iraki Jordan da sauransu, sun yi Allawadai da bude ofishin jakadancin Amurka a Quds.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar Aljazeera ta habarta cewa, mafi yawan wadanda aka gayyata zuwa tarin bikin bude ofsin jakadancin na Amurka sun yi watsi da gayyatar.

Sarkin kasar Jordan ya tuntubi Mahmud Abbas Abu Mazin ta wayar tarho, inda ya jaddada masa rashina mincewarsa da wannan mataki.

Haka nan kuma sauran kasashen duniya da dama da suka hada har da na turai duk sun yi tofin Allah tsine da wannan mataki.

A nata bangaren fira ministan kasar Birtaniya Theresa May ta bayyana cewa kasarta ba ta aniyar dauke ofishin jakadancinta zuwa Quds.

Ita ma Kuwait ta bukacia  gudanar da zama a kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya domin yin bahasi kan halin da ake ciki a Palastine da kuma kisan da Isra'ila take ta yi wa falastinawa ba ji ba gado.

Trump ya rubuta a shafinsa na twitter cewa, wannan babbar rana ce ga Isra'ila da ta shiga cikin tarihinta.

3714513

 

captcha