IQNA

An Raba Kwafin Kur’anai A Kasar New Zealand

23:54 - May 20, 2018
Lambar Labari: 3482676
Bangaren kasa da kasa, cibiyar da ke kula da ayyukan alhairi ta kasar hadaddiyar daular larabawa ta raba kwafin kur’ani mai tsarki a kasar New Zealand.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin jaridar alwatan cewa, cibiyar da ke kula da ayyukan alhairi ta kasar hadaddiyar daular larabawa ta Sheikh Maktum Rashid Al Makrum ta raba kwafin kur’ani mai tsarki da ma wasu littafan addini a kasar New Zealand da kuma wasu kasashen yankin.

Kur’anan da aka raba dai an tarjama su ne daga harshen laraci zuwa turanci, kuma an raba su a masallatai da kuma cibiyoyin adinin muslunci gami da makarantu.

Wannan ya zo ne a daidai lokacin da aka fara gudanar da ibadar azumin watan Ramadan mai alfarma, lamarin ya samu karbuwa matuka daga musulmin kasar.

3715924

 

 

 

 

 

 

 

captcha