IQNA

Firayi Ministan Malaysia Ya Ce Tattaunawa Da Trump Abu Ne Mai Wahala

23:49 - August 14, 2018
Lambar Labari: 3482891
Firayi ministan kasar Malaysia ya bayyana cewa tattaunawa da Trump abu ne mai matukar wahala domin a cikin sa’oi 24 zai iya canja ra’ayinsa.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na arabi 24 cewa, Mahatir Muhammad firayi ministan kasar Malaysia a zantawarsa da kamfanin dillancin labaran Associated Press ya bayyana cewa, tattaunawa da shugaban Amurka Donald Trump tana da wahala, saboda rashin tabbaci na ko zai iya tabbata kana bin da aka tattauna da shi.

Mahatir ya soke salon siyasar Donald Trump, tare da bayyana ta da cewa ba siyasa ce da za a iya dogaro da salonta ba, kuma Trump ba mutum ne da za a amince da abin da yake fad aba.

Dangane da batun halin da musulmin Rohingya suke ciki a kasar Myanmar kuwa, Mahatir ya bayyana shugabar kasar a matsayin babbar mai tauye hakkokin bil adama, inda sojojin gwamnatinta suka keta hurumin kabilar Rohingya da kuma yi musu kisan gilla.

 

3738525

 

 

captcha