IQNA

Mahajjata Sun Fara Shiga Mina Domin Fara Shirin Aikin Hajji

23:38 - August 19, 2018
Lambar Labari: 3482904
Bangaren kasa da kasa, mahajjata sun fara shiga Mina a yau domin fara shirin tarwiyyah inda hakan za a su yi tsayuwar arafah.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a  yau Lahadi maniyyatan suna fita daga birnin Makka zuwa Mina inda za su raya ranar “tarwiyyah’ gabanin wuce wa zuwa filin Arfaha a gobe Litinin inda za yi tsayuwar Arfaha da take a matsayin rukuni mafi girma na aikin Haji.

A gefe daya ma’aikatar harkokin cikin gidan Saudiyya ta sanar da cewa adadin maniyata da su ka isa kasar sun kai miliyan biyu.

Bugu da kari mahukuntan Saudiyyar sun sanar da kammala dukkanin shirye-shirye domin gudanar da aikin haji na bana.

Hajjin an bana dai yana daga cikin makamantansa ad suka gabata a cikin ‘yan shekarin nan da ke fuskantar kayyade maniyyata daga kasashen duniya daga bangaren masu rike da madafun iko a kasar Saudiyyah.

3739697

 

 

 

 

 

 

captcha