IQNA

Shirin Gwamnatin Kenya Na Koyar Da Kur’ani A Gidajen Kaso

23:56 - August 20, 2018
Lambar Labari: 3482909
Bangaren kasa da kasa, gwanatin kasar Kenya na da shirin fara koyar da kur’ani mai tsarkia  gidajen kaso ga musulmi.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, sakamakon matsaloli na addini da aka fuskanta a wasu lokutan baya a kasar Kenya, hakan ya sanya gwamnatin kasar yin shiri na koyar da ilmomin addini a gidajen kaso.

Wannan ya zo ne biyo bayan wata shawara da majalisar musulmin kasar Kenya ta bayar, wanda kuma gwamnatin kasar ta amince da ita.

Abin da shirin zai mayar da hankalia  kansa shi ne, ga musulmi wadanda ake tsare da su musamman ma wadanda aka samu da laifuka da suka danganci tayar da rikici da sunan addini, inda za a rika koyar da su kur’ani mai tsarki.

Baya ga haka kumaza a bayar da dama ga malamai su rika yi musu wa’azi da nasiha kan koyarwar adinin musulunci ta zaman lafiya da girmama juna tsakanin su da sauran mabiya addinai.

3739962

 

 

 

 

 

captcha