IQNA

Rouhani: Kafa Rundunar Amurka Ba Zai kawo Tsaro A Gabas Ta Tsakiya Ba

22:50 - August 15, 2019
Lambar Labari: 3483949
Shugaban Jamhuriyar musulunci ta Iran Hasan Rouhani ya ce duk maganganun da ake yi na kafa rundunar kawance a tekunFasha da tekun Oman zance ne kawai, bai tabbata ba, idan kuma hakan ya tabbata, ba zai taimaka ga tsaron yankin ba.

Kamfanin dillancin labaran iqna, yayin da ya jagoranci taron gwamnati a wannan Laraba, Shugaba Rouhani ya fadawa kasashen yankin tekun fasha cewa jamhuriyar musulunci ta Iran a shirye take ta kasance tare da kasashen wajen tabbatar da tsaro a wannan yanki mai daddaden tarihi, kamar yadda kuma ta kasance cikin wannan aiki cikin tsawon tarihi.

Rouhani ya tabbatar da cewa tsaron yankin tekun Fasha ba ya bukatar shigar dakarun kasashen ketare, don haka idan kasashen yankin suka hada kansu, suka kuma kasance a kusa da juna za su iya tabbatar da tsaron yankin ta hanyar tuntubar juna da tattaunawa ba tare da shigar dakarun ketare ba.

Sannan kuma ya tabbatar da cewa ikirarin kasar Amurka ba zai janyo wa yankin alhairi ba, domin a tsawon tarihi kasashen yankin sun kasance suna gudanar da mu’amala na ‘yan uwantaka da mutunta juna, idan har aka samu baraka ko rarrabuwar kawuna to shakka babu makiya ne za su amfana da hakan.

Yayin da ya koma kan haramtacciyar kasar Isra’ila, Rouhani ya ce ikirarin da ta yi na shiga cikin tsarin kawancen Amurka a tekun Fasha maganar wofi ce, domin idan har tana da karfin bayar da tsaro ga wani yanki, to ta yi kokarin kare kanta.

3834881

 

captcha