Kamfanin dillancin labaran iqna, an gudanar an gudanar da taron idin Ghadir a hubbaren Imam Ali tare da daukar tsauraran matakan tsaron a birnin.
Jami’an tsaron birnin Najaf sun sanar da cewa tun kafin wanan ranar an kammala daukar dukkanin matakan da suka dace domin tabbatar da tsaro a cikin da wajen birnin na Najaf.
Dubban daruruwan mabiya ahlul bait ne suka taru a hubbaren mai tsarki domin gudanar da wannan taro mai albarka, kamar yadda aka gudanar da ziyara a hubbaren da kuma makabartar Wadis Salam.