IQNA

‘Yan Sanda Sun Shiga Bincike Kan Cin Zarafin Wata Musulma a Ireland

23:51 - August 22, 2019
Lambar Labari: 3483975
Bagaren kasa da kasa, jami’an ‘yan sandan Ireland sun shiga gudanar da bincike dangane da cin zarafin wata musulma da wasu matasan yankin suka yi.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin jaridar Daily Sabah ya bayar da rahoton cewa, wasu matasa sun ci zarafin wata udurwa musulma ‘yar shekaru 14 a birnin Dublin na yankin Ireland.

Wasu da suka dauki ain abin ya faru a hoton bidiyo da suka saka a shafukan zumunta, hoton ya nuna yadda matasan suka cire lullubin da e kan wannan musulma suna izgili, kamar yadda kuma suka yi mata duka har ta fadi a kasa.

Wannan lamari ya fuskanci kakakusan martani daga sassa daban-daban na musulmia  Birtaniya da kasashen turai, tare yin yin kira ga mahukuntan Bitaniya da su dauki matakin gaggawa na gudanar da bincike kan wannan lamari.

Joseph Madigan ministan yada al’adu na Ireland ya bayyana cewa, suna yin tir da wannan mummunan aiki, kuma jami’an tsaro sun shiga gudanar da bincike domin gano wadannan matasa, domin su fuskanci hukunci.

Ali Salim wani mamba na cibiyar musulmin yankin Irelanda ya bayyana cewa, wannan abin da ya faru nuna wariya ne da kyama ga musulmi, kuma dole ne mahukuntan Ireland su dauki matakin bayar da kariya ga musulmi a yankin.

 

3836608

 

captcha