IQNA

Sakon Firayi Ministan Iraki Ga Masu Ziyarar Imam Hussain (AS)

23:51 - October 19, 2019
Lambar Labari: 3484169
Bangaren kasa da kasa, fira ministan Iraki ya isar da sako ga masu ziyarar arbaeen na Imam Hussain (AS).

Kamfanin dillancin labaran iqna, Adel Abdulmahdi firayi ministan Iraki ya isar da sako ga masu ziyarar arbaeen a wannan shekara, inda ya mika sakon jinjina a gare su da kuma yi a baki lale marhabin a kasar Iraki.

Fira ministan na Iraki ya bayyana taron ziyarar arbaeen a matsayin daya daga cikin manyan taruka da suke da musulmi a kasar Iraki, musamman a birnin Karbala inda hubbaren Imam Hussain yake.

Ya ce wannan babban abin alfahari ga dukkanin al’ummar Iraki, kamar yadda yay aba da irin hidimar da al’ummar kasar ta Iraki suke yi ga jama’a a yayin gudanar da wannan babban taro, wanda yake hada al’ummomi daga kasashe daban-daban na duniya a kan lamari guda, shi ne kaunar manzon Allah da iyalan gidansa.

A shekarar bana dai an bayyana adadin mutanen da suka halarci taron na arbaeen da cewa sun kai miliyan goma sha takawas, inda kusan miliyan uku sun fito ne daga kasashen duniya, yayin da sauran kuma sun fito ne daga sassa daban-daban na kasar ta Iraki.

3850888

 

 

captcha