IQNA

Cibiyar Azhar Ta Ce Masallacin Quds Na Larabawa Da Musulmi Ne

23:54 - May 16, 2020
Lambar Labari: 3484805
Tehran (IQNA) Cibiyar Musulunci ta Azhar da ke kasar Masar ta sanar da cewa birnin Quds zai ci gaba da kasaencewa na larabawa da musulmi, kuma mamayarsa ba za ta dawwama ba.

Tashar RT ta bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da cibiyar Azhar ta fitar dangane da cikar shekaru 72 da yahudawan sahyuniya suka mamaye Falastinu, ta bayyana cewa birnin Quds zai ci gaba da kasancewa na al’ummomin musulmi da larabawa har abada.

Bayanin ya ce, tun bayan mamayar yahdawa a Palestine, ya zuwa yanzu dubban gidagen falastinawa aka rushe baki daya, kuma aka canja wa yankuna da biranensu fasali tare da mayar da su na yahudawa.

Haka nan kuma a cikin wadannan shekaru Isra’ila ta kori fiye da kashi 85 cikin dari na Falastinawa daga kasarsu, inda suka koma suna rayuwa a cikin kasashe da ke makwabtaka da Falastinu.

Bayanin na Azhar ya ce wannan shi ne abin kunya da zalunci mafi muni da aka aikata a cikin wannan karni, musamamn ma yadda wanann zalunci da abin kunya zama halastacce karbabbabe a hukumance a wurin kasashen duuniya.

Daga karshe Azahar ta kirayi sauran kasashe da al’ummomi masu sauran lamiri da su sauke nauyin da ke kansu wajen kare hakkokin al’ummar Palastinu da suke rayuwa a cikin mawuyacin hali tsawon shekaru 72 a jere.

 

https://iqna.ir/fa/news/3899124

 

 

 

captcha