Shafin yada labarai na arab news ya bayar da rahoton cewa, sakamakon wani shirin gwamnati na gina wata babbar gada da za ta ratsa a cikin wata tsohuwar makabarta a cikin alkahira, ana ta cece ku ce a shafukan zumunta a kan wannan shiri.
Bayanin ya ci gaba da cewa, an kaddamar da wani kamfe yanzu haka a shfukan sada zumunta musammana facebook domin kalubalantar wannan shiri na gwamnatin kasar Masar.
Hesham Auf daya ne daga cikin masana lamarin tarihi a kasar Masar ya bayyana cewa, an saka wannan makabarta da aka gina sama da karni biyar da suka gabata a cikin wuraren tarihi na duniya a 2009, saboda haka rusa wannan wuri ya saba wa dokoki na duniya.
Sai dai Usama Tal’at shugaban bangaren gudanar da bincike kan wuraren tarihi a jami’ar Egypt-Japan University of Science and Technology, ya bayyana cewa abin da ake yadawa ba gaskiya ba ne, wannan wuri baya daga cikin wuraren tarihi na duniya.