IQNA

Tarayyar Afirka Za Ta Iya Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Taka Wa Isra’ila Burki

19:05 - February 23, 2021
Lambar Labari: 3485682
Tehran (IQNA) Na’emm Jeenah malami ne a jami’ar Johannesburg a kasar Afirka ta kudu wada ya bayyana cewa kungiyar tarayyar Afirka za ta iya takawa Isra’ila burki ta hanyoyi da dama.

A zantawar da ta hada shi da kamfanin dillancin labaran iqna, Na’eem Jeenah ya bayyana cewa, gwamnatin yahudawan Isra’ila tana neman hanyar samun wurin zama  a cikin kasashen Afirka ta hanyoyi daban-daban, wanda kuma kasashen Afirka da suke da masaniya kan irin ta’asar da take tafkawa, ba za su mika mata kai ba.

Ya ce tun bayan da Isra’ila ta mika bukatar neman zama daya daga cikin ammbobin ‘yan kallo a kungiyar tarayyar Afirka, kasashen Afirka da dama suka nuna rashin gamsuwa da hakan, wanda hakan ke nuni da cewa mutanen Afirka sun san abin da suke yi.

Jeenah ya ci gaba da cewa, sakamakon irin mulkin mallaka da zalunci da mutanen Afirka suka fuskanta daga kasashen turai, wannan yasa sun samu masani kan irin illar da take tatatre da zalunci da danne al’umma da nuna musu fin karfi, wanda kuma shi ne abin da Isra’ila take yi a kan al’ummar Falastinu.

Ya ce duk da cewa kasashe d dama Afirka suna da hulda ta diflomasiyya da Isra’ila, amma za su iya daukar matakin ladabtar da ita ta hanyar rage karfin wannan hulda da ke tsakaninsu, kuma za su iya yin hakan.

Ya bayar da misali da kokarin Isra’ila na neman zama mamba mai sanya ido a kungiyar tarayyar Afirka, a maimakon haka sai kasashen Afirka suka fitar da wani kudiri na nuna cikakken goyon bayansu ga al’ummar falastinu, tare da yin kira ga Isra’ila da ta kawo karshen mamayar zalunci da ke yi a kan yankunan Falastinawa.

3955323

 

captcha