Karatun kur'ani mai tsarki tare da shekh Anwar Shuhat, wanda shi ne babban dan marigayi Sheikh Muhammad Shuhat Anwar, fitaccen makarancin kur'ani dan kasar Masar.
A Cikin wannan faifan bidiyon yana karanta ayoyi na 17, 18, 19 a cikin surat Infitar, a cikin kyakkyawan sauti na tilawa.
darul kur'an da ke karkashin cibiyar Imam Ali (AS) da ke birnin Hamburg na kasar Jamus ne ke saka wadannan hotunan bidiyo na karatun kur'ani daga makaranta kur'ani daga sassa na duniyar musulmi.