IQNA

Wata Yarinya 'Yar Shekaru 16 Mai Matsalar Kwakwalwa Ta Hardace Dukkanin Kur'ani

23:57 - June 09, 2021
Lambar Labari: 3485997
Tehran (IQNA) wata yarinya 'yar shekaru 16 da ke da matsalar da ta shafi kwakwalwarta a kasar Jordan ta hardace dukkanin kur'ani mai tsarki.

Shafin yada labarai na Roya News ya bayar da rahoton cewa, Rawan Duwaik yarinya ce 'yar shekaru 16 da ke da matsalar da ta shafi kwakwalwarta a kasar Jordan, amma kuma ta samu nasara wajen hardace dukkanin kur'ani mai tsarki.

Mahaifiyar Rawan ita ce ta ke koyar da ita, tana karfafa ta, kuma tana yawan karanta mata kur'ani da maimaita ayoyinsa a gabanta, wanda hakan ya ba ta damar hardace dukkanin abin da mahaifiyarta ke karanta mata, da farkon kur'ani har zuwa karshensa.

Rawean Duwaik ta samu nasarar hardace dukkanin kur'ani mai tsarki ne a cikin shekaru bakawai.

 

 

3976301

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kasar Jordan
captcha