IQNA

Ayyukan Cibiyoyi Da Bankunan Musulunci Na Samun Karbuwa A Najeriya

19:29 - December 13, 2021
Lambar Labari: 3486680
Tehran (IQNA) ​Bankunan Najeriya na da sha'awar gudanar da ayyukansu a duniya, wanda hakan ke kara habaka kyakkyawar alaka da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi na duniya da ke bayar da hidimomin kudi na Musulunci.

A rahoton kamfanin dillancin labaran iqna, Sauye-sauyen tattalin arzikin Najeriya da karbuwar kimar da hukumomin kididdiga na duniya suka yi sun inganta makomar tattalin arzikin Najeriya a matsayin wurin zuba jari mai inganci.

Ko da yake har yanzu ba a amince da tsarin ba da tallafin kudi na Musulunci a hukumance ba a wasu kasashe na duniya, amma irin karfin da aka amince da shi da ayyukan cibiyoyi da bankunan da ke aiki a cikin wannan tsarin hada-hadar kudi, ya sanya gwamnatoci da masu tsara manufofin tattalin arziki na kasashe da dama suka gamsu da shi.

A Nahiyar Afirka, wacce ta fi dacewa ga masu zuba jari saboda dimbin  arziki da Allah ya huwace nahiyar da kuma yanayi na zamantakewar al'umma, tsarin samar da kudade na Musulunci yana bunkasa a nahiyar.

Najeriya na daya daga cikin kasashen da suka zama cikin cibiyoyin tattalin arziki da kasuwanci a nahiyar Afirka sakamakon bunkasar tattalin arzikinta, kuma a halin da ake ciki, hidimomin cibiyoyin kudi na Musulunci yana taka rawa sosai wajen wannan ci gaban.

Sai dai hasashen tsarin samar da kudade na Musulunci a Najeriya ya fito karara.

Ci gaban tattalin arzikin kasar, wanda ya sanya ta zama cibiyar masu zuba jari daga kasashen duniya, duk da matsalolin da aka samu sakamakon bullar cutar corona, tattalin arzikin Najeriya ya habaka musamman idan aka yi la’akari da karuwan kudadenta na asusun ajiya da ke waje.

Haɓaka tsarin bayar da kuɗi bisa tsarin cibiyoyin hada-hadar kudade na Musulunci a wannan ƙasa zai haifar da babbar dama ta jawo hannun jari daga masu zuba jari na cikin gida da na waje, kuma a ƙarshe zai haifar da haɓakar tattalin arziƙi da ingantattun ayyuka.

 

4020287

 

captcha