IQNA

Yahudawa Hana Kiran Salla A Masallacin Annabi Ibrahim

15:55 - May 05, 2022
Lambar Labari: 3487253
tehran (IQNA) A ci gaba da cin zarafin musulmi da yahudawan sahyuniya ke yi a cikin yankunan Falastinawa da suka mamaye, tun a jiya Laraba sun sanar da hana yin kiran salla a cikin masallacin annabi Ibrahim amincin Allah ya tabbata a gare shi da ke birnin Alkhalil.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, daruruwan yahudawan sahyuniya ne masu tsatsauran dad a wadanda sojoji da ‘yan sanda gwanatin yahudawan Isr’ila ke marawa baya suka kutsa kai a cikin masallacin a  yau tare da keta alfarmarsa.

Wasu rahotannin kuma sun ce wasu gungun sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila da yahudawa 'yan kaka-gida sun kutsa kai cikin harabar masallacin Al-Aqsa da ke tsohon birnin Quds da aka mamaye tare da yin arangama da musulmin Palasdinawa masu ibada,  a wani mataki na wuce gona da iri kan wannan wuri mai tsarki.

Dakarun mamaya na haramtacciyar kasar Isra'ila sun kai hari a masallacin al-Aqsa a matsayin wuri na uku mafi tsarki ga musulmi a duniya a ranar yau Alhamis, inda suka yi ta harbe-harbe da gurneti da harsasai na roba kan masu ibada, a daidai lokacin da ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula a lokacin da ake cika shekaru 74 da yahudawan Sahyuniya suka mamaye Falastinu.

Ranar Nakba tana nufin bukin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta sanar da kasancewarta a yankunan Falasdinawa da ta mamaye a tsakiyar watan Mayun shekara ta 1948, tare da korar dubban daruruwan Falasdinawa daga kasarsu ta haihuwa. Isra'ilawa na bikin ne a ranar 4-5 ga Mayu na wannan shekara.

An sanya ranar Nakba a matsayin ranar 15 ga Mayu a kowace shekara, amma Isra'ilawa na bikin abin da suka kira ranar 'yancin kai daidai da kalandar Ibrananci, kasantuwar kwanan watan kalandar Gregorian ta sabawa ta Ibrananci.

Sojojin Isra'ila sun far wa Musulmai masu ibada tare da fatattakarsu don ba wa yahudawa ‘yan share wuri zauna damar shiga wurin mai tsarki bayan da suka farfasa daya daga cikin kofofinsa.

Kafofin yada labaran Falasdinu sun ce sojojin Isra'ila sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa Falasdinawa a wurin. Akalla masu ibada 12 ne suka jikkata yayin da wasu da dama suka shake bayan shaker hayaki mai sa hawaye.

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4054839

 

 

 

captcha