IQNA

Batun Neman A Dakatar Da Gine-Ginen Isra’ila A Gaban Kwamitin Tsaro / Veton Amurka Na Hanya

20:09 - December 22, 2016
Lambar Labari: 3481059
Bangaren kasa da kasa, an gabatar da daftarin kudiri gaban kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya da ke neman haramtacciyar kasar Isra’ila ta dakatar da gina matsugunnan yahudawa a yankunan Palastinawa.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadrawa na tashar alalam cewa, a yau za a tattauna wannan daftarin kudiri, wanda ya bayyana ayyukan ginin matsgunnan yahudawa a cikin yankunan da cewa ya sabawa dukkanin dokoki na kasa da kasa.

Daftrain kudirin ya yi kira ga haramtacciyar kasar Isra’’ila da ta kawo karshen dukkanin ayyukan mamaya a cikin yankunan palastinawa da gina matsugunnai a dukkanin yankunan har da gabachin birnin Quds.

Har yanzu dai Amurka ba ta ce uffan kan wannan daftarin kudiri wannan kada kuri’a a kansa, amma dai bisa ga alada duk wanmi daftarin kdiri da ya soki Isra’ila ko mkuma wani aikin barna da take, Amurka tana kare shi ido rufe.

3555826


captcha