IQNA

Dokar Hana Saka Hijabi A Sink Yand Da Ke China

23:56 - March 31, 2017
Lambar Labari: 3481364
angaren kasa da kasa, mahukunta a kasar na shirin daukar matakai na hana saka hijabin muslunci a yankin Sink Yang na kasar China.

BKamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin jaridar Independent cewa, mahukuntan kasar China sun kudiri aniyar daukar matakai na takura ma mabiya addinin muslunci a wasu yankunan kasar

Daga cikin irin matakan da suke dauka akwai hana saka hijabi a cikin wuraren jama'a da sauran wuraren aiki, inda za a tilasta musulmi da su saka kaya ba tare da lullubi ba kamar yadda suka saba.

Haka nan kuma akwai batun kayyade iyali, wanda doka nea kasar kan cewa mutane su kayyade dadin iyalansu, amma wannan doka ba ta shafi musulmi ba, amma kuma yanzu dokar za ta hada har da mabiya addinin musluncia yankunansu.

A cikin shekarun da suka gabata, mahukuntan kasar China sun kafa dokar hana musulmi masu aiki yin azumi, saboda abin da suka kira da cewa rauni da azumi ke sanya sua lokacin aiki.

Yanzu haka dai musulmin kasar ta China suna korafi kan wannan doka, wadda suke kallonta a matsayin keta 'yancinsu na yin addini.

3586175

captcha