IQNA

An Banka Wa Cibiyar Musulmi Wuta A Kasar Sweden

23:09 - May 01, 2017
Lambar Labari: 3481456
Bangaren kasa da kasa, wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba sun banka wa babbar cibiyar musulmi da ke birnin Stockholm na Sweden wuta.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na imamalicenter.es cewa, a daren jiya wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba sun cinna wuta akan ginin cibiyar wanda ke hade da babban masallaci, inda wani bangaren ginin cibiyar tare da masallacin suka kone.

Bayanin ya ce ba a samu asarar rai ko jikkata ba, amma dai kaddarorin da ke cikin cibiyar da masallacin sun kone.

Jami’an tsaron kasar birnin Stockholm sun ce bas u kama kowa a kan wannan laifi ba, amma dai suna gudanar da bincike domin gano wadsanda suke da hannu a cikin wannan aika-aikata.

Kyamar musulmi na karuwa a cikin kasashen turai a cikin lokutan nan, sakamakon hare-haren ta’addanci da ‘yan takfiriyya ke kaiwa da sunan jihadi.

3595007









An Banka Wa Cibiyar Musulmi Wuta A Kasar Sweden

An Banka Wa Cibiyar Musulmi Wuta A Kasar Sweden

An Banka Wa Cibiyar Musulmi Wuta A Kasar Sweden

captcha