IQNA

Isra'ila Ta Hana Gudanar Da Sallar Juma'a A Cikin Masallacin Quds

17:40 - July 14, 2017
Lambar Labari: 3481698
Bangaren kasa da kasa, Sakamakon musayar wutar da aka yi yau tsakanin Palastinawa 'yan gwagwarmaya da kuma jami'an 'yan sanda yahudawan sahyuniya a bakin kofar masallacin Quds, Isra'ila ta sanar da hana sallar Juma'a a yau a cikin masallacin.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga kamfanin dilalncin labaran PNN ya bayar da rahoton cewa, sakamakon cin zarafin da musulmin Palastinu ke fuskanta a kowace rana ta Juma'a ahannun jami'an tsaron yahudawan Isra'ila, a yau wasu Palastinawa sun uku sun yi dauki ba dadi da 'yan sandan Isra'ila a bakin kofar shiga masallacin Quds, inda suka halaka 2 daga cikin 'yan sanda Isra'ila, tare da jikkata wani, yayin da su kuma suka yi shahada.

Jim kadan bayan faruwar lamarin, Haramtacciyar kasar Isra'ila ta sanar da hana gudanar da sallar Juma'a a cikin masallacin mai alfarma, tare da baza jami'an soji da 'yan sanda a ciki da wajen masalalcin da kuma hanyoyin da ke zuwa masallacin, domin tabbatar da an hana gudanar da sallar juma'a acikin masallacin.

Wanann dai shi ne karon farko da haramtacciyar kasar Isra'ila ta hana gudanar da sallar Juma'a baki daya a cikin masallacin tun daga shekarar 1969, duk da cewa ta kan kayyade shekarun mutanen da za su yi sallar Juma'a a cikin wannan masallaci a wasu lokuta, inda takan kayyade mutane masu shekaru arba'in zuwa hamsin abin ya yi sama, da cewa su kadai za su sallar Jumaa a cikin masallacin mai alfarma.

3618660


captcha