IQNA

Masallacin Aqsa Na Ci Gaba Da Kasancewa Karkashin Mamaya

20:21 - July 17, 2017
Lambar Labari: 3481707
Bangaren kasa da kasa, Palasdinawan sun ki bi ta karkashin kofar na bincike domin shiga masallacin kudus yayin da wani daga cikin masu gadin wurin ya yi kiran salla a wajen masallacin.
Kamanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, yan sahayoniyar dai sun kafa kofar ne ta binciken mutane a bakin masallacin Kudus bisa abinda su ka kira dalilai na tsaro, kwana biyu bayan da su ka hana yin sallar juma'a a cikin masallacin.

Al'ummar Palasdinu tana nuna rashin amincewarta da matsin lambar da ake yi musu a duk lokacin da su ke son shiga masallacin.

Wannan mataki dai yana zuwa ne sakamakon yadda wasu daga cikin gwamnatocin larabawa suke ci gaba da nuna halin ko in kula da ta'addancin Isara'ila a kan wurare masu tsarki da suka hada da masallacin aqsa alkiblar musulmi ta farko.

Haramtacciyar kasar Isra'ila na ci gaba da cin karenta babu babbaka a kan wannan wuri mai tsarki ne tare da hana musulmi yin salla ta hanyar kafa musu ka'idoji masu tsauri da cin zarafinsu, wanda hakan yasa ala tilas musuli suke ci gaba da kauarace ma yin salla a cikin masalalci, duk kuwa da cewa a jiya yahudawan sun sanar da bude shi, tare da bayar da damar shiga ciki bisa sharadin da suka gindaya.

3619960

Masallacin Aqsa Na Ci Gaba Da Kasancewa Karkashin Mamaya


captcha