IQNA

Fiye Da Mutane Dubu 25 Ne Suka Yi Sallar Juma’a A Masallacin Aqsa

23:55 - August 04, 2017
Lambar Labari: 3481767
Bangaren kasa da kasa, duk da irin matakan takurawa da cin zarafin da haramtacciyar kasar Isr’ila ta dauka a masallacin Aqsa masallata fiye da dubu 25 ne suka yi salla a yau a cikin masallacin.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ma’a cewa, tun kimanin makonni uku kenan jami’an tsaron yahudawan Isra’ila suka hana yin salla wannan massalaci, amma duk da irin matakan takurawa da cin zarafin da haramtacciyar kasar Isr’ila ta dauka a masallacin musulmi fiye da dubu ashirin da biyar ne suka yi salla a yau a cikin masallacin mai alfarma.

Sheikh Muhammad salim Muhammad Ali limamin masalalcin Aqsa ya bayyana yau a cikin hudubar juma’a cewa, wannan masallaci mallakin msuulmi ne, saboda haka ba zasu taba amince wani bangare da ban a musulmi bay a jagoranci sha’anin wannan masallaci ba.

Tun bayan harin da wasu matasa suka kaddamar kan yahudawan sahyuniya kimanin makonni uku da suka gaba a kusa kofofin wannan masallaci, sakamakon cin zarafin da jami’an tsaron yahudawa suke yi wa musulmi, tare da kasha biyu da cikin jami’an tsaron yahudawa, Isra’ila ta dauki matakan hana salla a masallaci.

Sai dai bayan da ta fuksnaci matsin lamba daga kasashen duniya, ta sassauta matakan da ta dauka abaya, inda a yau musulmi sun samu sun yi salla a cikin masallacin, duk kuwa da cewa addadinsu bai kai koda rabin abin da aka saba gani ba.

3626676


captcha