IQNA

An Gano Wani bam Da Ke Shirin Tashi A Cikin Masu Makoki A Iraki

22:44 - September 23, 2017
Lambar Labari: 3481924
Bangaren kasa da kasa, jami'an tsaron kasar Iran sun samu nasara gano wani bam da aka dana da nufin tayar da shi a tsakiyar masu makoki.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na shafaqna cewa, a jiya , jami'an tsaron kasar Iran sun samu nasara gano wani bam da aka dana da nufin tayar da shia tsakiyar masu makoki na Ashura, wanda aka fara daga jiya.

Bayanin yace tun bayanda aka fara tarukan makokin ajiya, jami'an tsaro suke ci gaba da yin sintiri musammana wuraren da aka fara gudanar da tarukan na watan muharram kamar yadda aka saba.

Yan ta'adda wadnda a halin yanzu sun rauni matuka sakamakon irin matakan da jami'an tsaron Iraki suka dauka na fuskantarsu da karya lagonsu a cikin wasu lardunan kasar, a halin yanzu sun sun son su yi amfani da damar domin ganin sun dauki fansa akan masu gudanar da tarukan makoki.

A nasu bangaren jami'an tsaron na Iraki suna ci gaba da daukar dukkanin matakai aa cikin birnin Bagadaza da sauran birane da ake gudanar da tarukan Ashura.

3645328


captcha