IQNA

Tattauna Hanyoyin Taimaka Ma yara Ta Fuskar Kur'ani A Senegal

19:42 - October 25, 2017
Lambar Labari: 3482037
Bangaren kasa da kasa, an tattauna kan hanyoyin da ya kamata a bi domin taimaka ma kananan yara masu sha'awar karaun kur'ani a Senegal.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, jami'an karamin ofishin jakadancin Iran a Senegal sun tattauna kan hanyoyin da ya kamata a bi domin taimaka ma kananan yara masu sha'awar karaun kur'ani a Senegal tare da wasu daga cikin shugabannin cibiyoyin addini.

Bayanin ya ci gaba da cewa, muhimamn lamurran da tattaunawar ta mayar da hankalia kansu sun hada da samar da kayan aiki wajen koyarwa a makarantun kur'ani, da kuma taimaka ma malamai masu koyar da yara karatun kur'ani.

Karamin ofishin jakadancin Iran a Senegal ya bayar da wasu daga cikin kayayyakin da makarantun Islamiyya suke bukata a sassa daban-daban na kasar, tare da hadin gwiwa da ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar.

Kasar Senegal na daga cikin kasashen musulmia nahiyar Afirka da suke mayar da hankali matuka kan lamarin kur'ani mai tsarki, da kuma himma wajen ganin ci gaban addinin musulunci a kasar.

Mabiya darikun sufaye su ne suka fi yawa a kasar Senegal, wanda hakan ya sanya lamarin sufanci da kuma tsakake ruhi yake da babban tasiri.

3656797


captcha