IQNA

MDD Ta Nuna Damuwa Kan Tsare Kananan Yara Palastinawa Da Isra'ila Take Yi

16:39 - November 07, 2017
Lambar Labari: 3482077
Bangaren kasa da kasa, Majalisar dinkin duniya ta damuwarta kan yadda haramtacciyar kasar Isra'ila take kame kananan yara Palastinawa tare da tsare su.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Palastine cewa, Farhan Haq kakakin majalisar dinkin duniya ya bayyana cewa, halin da kananan yara Palastinawa suke ciki a kurkukun Isra'ila yana da ban takaici.

Ya ci gaba da cewa yanzu haka akwai kananan yara fiye da 500 a cikin gidajen kason Isra'ila da suke rayuwa a cikin mawuyacin halin.

Ya ce ya zama wajibi Isra'ila ta girmama dokokin duniya, ta daina kama kananan yara tana tsare a gidajen kurkuku a matsayin fursunoni, domin hakan ya yi hannun riga da dukkanin dokoki na duniya, kuma ta gaggauta sakin wadanda take tsare da su.

3660912


captcha