IQNA

Musulmin Amurka Za Su Gudanar Da Sallar Jam'i A Gaban Fadar White House

22:18 - January 24, 2018
Lambar Labari: 3482332
Bangaren kasa da kasa, musulmin kasar Amurka na shirin gudanar da sallar zuhur a cikin jam'i a gaban fadar white house a ranar Asabar mai zuwa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na CAIR cewa, a ranar Asabar mai zuwa , musulmin kasar Amurka na shirin gudanar da sallar zuhur a cikin jam'i a gaban fadar white house, domin nuna rashina mincewa da irin matakan da Trump yake dauka na nuna kyama ga msuulmi.

A cikin bayanin da cibiyar ta fitar, ta bayyana cewa za a gudanar da wani gagarumin jerin gwano a cikin birnin Washington, wanda zai kare a gaban fadar white house a ranar Asabar, kuma za a yi sallar zuhur a cikin jam'i, daga nan kuma za a yi bayani.

Babban abin da bayanin zai mayar da hankali a kansa shi ne rashin amincewa da matakan nuna wariya da kyama da shugaban kasar Amurka Donald Trump yake nuna wa musulmi a kasar a hukumance.

Bisa tsarin Amurka dai kowa yana da hakkin ya yi addininsa daidai da fahimtarsa da kuma abin da ya yi Imani da shi, ba tare da wani ya yi masa katsalandan ko cin zarafinsa ba.

Abin da Trump yake na wulaknta msuulmi ya yi hannun riga da abin da ke cikin kundin tsarin mulkin kasar Amurka, kuma hakan cin zarafin bil adama ne, wanda akansa kawai ya kamata Trump ya sauka daga shugabancin kasar, saboda bai mutunta kundin tsarin mulkinta ba.

3684997

 

 

captcha