IQNA

Taron Kammala Gasar Kur’ani A Kasar Senegal / An Gayyaci Iran

22:47 - February 27, 2018
Lambar Labari: 3482435
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da taron rufe gasar karatun kur’ani mai tsarki a kasar Senegal tare da halartar manyan jami’an gwamnati da na diflomasiyya.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren hulda da jama’a na cibiyar yada al’adun muslunci cewa,  Sayyid Hassan Esmati , shugaban ofishin kula da harkokin al’adu na Iran a Senegal ya bayyana cewa, za a gudanar da taron rufe gasar karatun kur’ani mai tsarki a kasar Senegal tare da halartar manyan jami’an gwamnati da na diflomasiyya da suka hada har da na kasar Iran.

Daga cikin manyan bakin da za su halarci taron rufe wannan gasa har da Macky Sall shugaban kasar ta Senegal, wanda zai kasance daga cikin wadanda za su mika kyautuka ga wadanda suka nuna kwazo a gasar.

Wannan gasa ana gudanar da ita a kasar Senegal a kowaces hekara, kuma tana samun halartar makaranta daga dukkanin sassa na kasar, kamar yadda kuma akan gayyaci wasu daga cikin makaranta daga kasshen yammacin nahiyar Afirka.

3695167

 

 

 

 

 

 

 

 

captcha