IQNA

An Gargadi Yahudawan Sahyuniya Kan Keta Alfamar Masallacin Quds

23:12 - March 25, 2018
Lambar Labari: 3482508
Bangaren kasa da kasa, ma'aikatar kula da harkokin addini ta Palastinu ta gargadi yahudawan sahyuniya dangane da shirin gudanar da bukukuwan idin yahudawa a cikin masallacin Quds.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na arabi21 ya habarta cewa, , ma'aikatar kula da harkokin addini ta Palastinu ta gargadi yahudawan sahyuniya dangane da shirin gudanar da bukukuwan idin yahudawa a cikin masallacin Quds mai alfarma.

Bayanin ya ce tun kimanin shekaru hamsin da suka gabata ne bayan kafa ne yahudawan haramtacciyar kasar Isra'ila suka fara gudanar da tarukan idin yahudawa a gefen masallacin Quds, a shekarar bana kuma suna nufin gudanar da shi a cikin masallacin mai alfarma.

Bisa ga al'ada mnyan malaman yahudawa da kuma wasu daga cikin yahudawa masu tsatsauran ra'ayin sahyuniya ne suke halartar wannan idi, tare da rakiyar daruruwan jami'an tsaron Isra'ila da suke ba su kariya.

Ma'aikatar kula da harkokin addini ta Palastinu ta ce yahudawa suna yin amfani da wannan damar domin keta alfarmar wurare masu tsarki na musulmi da kiristoci musamman masallacin Quds mai alfarma, wanda kuma yin wadannan bukukuwa a cikin wannan masallaci zai fuskanci fushi daga al'ummar Palastinu da ma dukkanin musulmi na duniya.

3701828

 

 

 

 

captcha