Kamfanin dillancin labaran iqna, shugabar hukumar kare hakkin bil'adam ta Majalisar Dinkin Duniya Michelle Bachelet ta fada a jiya Talata cewa; Idan 'Yan Rohinga su ka koma gida a yanzu, to rayuwarsu za ta fuskanci hatsari.
Bachelet ta ci gaba da cewa; A kodayaushe hukumar kare hakkin bil'adaman ta Majalisar Dinkin Duniya tana samun rahotanni akan yadda ake ci gaba da cutar da azabtar da kuma sace 'yan Rohinga a can kasar Myanmar.
A shekarar da ta gabata hukumar kare hakkin bil'adaman ta Majalisar Dinkin Duniya ta zargi sojojin kasar Myanmar da hannu a yi wa al'ummar musulmin kasar kisan kiyashi, sannan ta bukaci da a hukunta janar-janar guda biyu na kasar.
Fiye da musulmin Rohinga dubu shida ne masu tsauran ra'ayin addinin Bhuddah suka kashe a kasar ta Mayanmar tare da tilasta wa wasu da adadinsu ya kai miliyan guda yin hijira.