IQNA

China Ta Bayyana Musulmin Uyghur A Matsayin Babbar Barazana ga Kasar

21:16 - December 21, 2018
Lambar Labari: 3483238
Bangaren kasa da kasa, Gwamnatin kasar China ta bayyana musulmin Uyghur a matsayin babbar barazana a gare ta, inda take danganta su da ayyukan ta'addanci.

Kamfanin dillancin labaran iqna, ya byar da rahoton cewa, a ci gba da takura ma musulmi 'yan kabilar Uyghur da gwamnatin kasar China ke yi, ta bayyana su a matsayin babbar barazana ga makomar kasar.

Kasar ta China ta ce musulmin Uyghur da ke yankin Xin Kiyang ba su magana da harshen China ba, sai dai harshen kabilarsu, kuma ba su da kwarewa a cikin kowane irin lamari na ci gaban kasa, saboda haka suke karkata ga kungiyoyin 'yan ta'adda.

Tun kafin wannan lokacin dai gwamnatin kasar China ta jima tana takura ma musulmi wannan yanki, da ma musulmi na wasu yankunan kasar, inda takan hana su gudanar da wasu ayyukansu na ibada, da hakn ya hada har da yin azumi, bisa hujjar cewa azumi yana sanya lalaci da kasala, ta yadda musulmi ba su iya yin aiki kamar sauran mutane da ba su yin azumi, saboda haka gwamnati ke hana musulmi masu zuwa aiki yin azumi.

3774289

 

 

 

captcha