Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar rahoton cewa, Huza Ali Amnasuri dan kasar hadaddiyar daular larabawa UAE, na shirin tafiya zuwa sararin samaniya a cikin watan Satumba mai zuwa.
Kasantuwar wannan mutum musulmi ne, wani kamfani mai suna Space Food Laboratary ya shirya abinci na musamman wanda wannan mutum zai yi amfani da shia sararin samaniya.
A cikin shekara ta 2018 ce hadadiyar daular larabawa ta kulla wata yarjejeniya tare da Rasha kan zuwa sararin samaniya.
Amansuri tare da wani mutum mai suna Sultan Niyadi dukkaninsu ‘yan kasar hadaddiyar daular larabawa, su ne suka bukaci tafiya zuwa sararin samaniya.
Tuna cikin shekarar da ta gabata ne suka samu horo na zuwa sama, amma Almansuri ne shi ne ya samu sa’ar dacewa, inda zai yi kwanaki takwas a sama kafin ya dawo kasa.