Kamfanin dillancin labaran iqna, ya nakalto daga shafin Al’ayi cewa, jami’an ‘yan sanda kasar Norway, sun bayyana cewa harin da wani mutum ya kai a masalalcin Nura cikin birnin Oslo fadar mulkin kasar, aiki ne ta’addanci.
Roney Scold babban jami’in ‘yan sanda a kasar Norway ya bayyana, cewa, masu tsatsauran ra’ayin kin jinin baki a kasar Norway ne suka kai hari a kan masalalcin Nur, wanda wuri ne na ibadar musulmi.
Ya ce ko alama rudunar ‘yan sanda ta kasar ba za ta yi saku-saku da ayyuka irin wadannan ba, domin kuwa ayyuka ne na ta’addanci bisa dokar kasar.
A jiya ne wani mutum ya shiga masalalcin Nur da ke Osloa kasar ta Norway ya bude wutar bindiga, amma bai kashe kowa ba.