Shafin jaridar Yaum Sabi ya bayar da rahoton cewa, ministan ma’aikatar kula da harkokin addinai na kasar Masar Muhammad Mukhtar Juma’a ya ce; za a gudanar da zaman taron karawa juna sani na malamai da masana na addinan muslunci da kiristanci nan ba da jimawa ba.
Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da shugabannin mabiya addinin kirista a lardin Asyut na kasar Masar, a wata ziyarar aiki da ya kai a lardin.
Ya ci gaba da cewa abu ne da ya zama wajibi a zauna lafiya tare da fahimtar juna tsakanin dukkanin mabiya addinai, kuma musulmi da kirista ba su da wata matsala ta rayuwa tare a tsawon tarihi, kuma shi ne da yake da muhimamnci a ci gaba da tabbatar da shi.
Bayan haka kuma ministan ya kai ziyara a masallacin Dirut, wanda yake da tsohon tarihia kasar ta Masar, inda a halin yanzu ake batun sake gyaran masallacin.
Haka nan kuma ya bukaci masu kula da masallacin das u dauki matakan ad suka dace domin kiyaye ka’idoji na kiwon lafiyar al’umma, musamman kasantuwar masallacin wuri ne na taruwar mutane da dama.