IQNA

Iran Ta Ce Dole Ne A Hukunta Jami’an Isra’ila Kan Kisan Kiyashin Da Suka Yi A Falastinu

23:13 - May 22, 2021
Lambar Labari: 3485938
Tehran (IQNA) Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bayyana nasarar  al’ummar Gaza a kan yahudawa da cewa, nasara ce ta al’umma baki daya.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fitar da wani bayani a yau, inda ta bayyana nasarar da al’ummar Gaza suka samu a karawarsu da yahudawan sahyuniya da cewa, nasara ce ta al’umma baki daya.

A cikin bayanin, ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ta bayyana cewa, a cikin kwanaki goma sha daya da Isra’ila ta kwashe tana kaddamar da yaki a kan al’ummar Gaza da sauran yankunan Falastinawa, ba ta iya cimma komai ba, sai dai rusa gidajen jama’a da wuraren ibada da cibiyoyin kasuwanci, da kisan mata da kananan yara da fararen hula.

Bayanin ya ce wanann gazawa ce ba jarunta ko bajinta ba, kamar yadda Firayi minstan Isra’ila Benjamin Netanyahu ke ta babatu kan cewa ya samu nasara a yakin da ya kaddamar kan al’ummar Gaza, inda a cewarsa ya ragargaza karfin da Hamas da sauran kungiyoyin gwagwarmayar Falastinawa suke da shi.

Haka nan kuma bayanin na ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa, dole ne a karfafa al’ummar falastinu, a kara kyautata karfin ariya da suke da shi domin su kare kansu daga duk wani shishigi na yahudawan sahyuniya.

Iran ta bayyana cewa yanzu ta shirya wasu kayan taimako da za ta tura zuwa yankin zirin Gaza, da suka hada da mahunguna, da abinci da sauran kayayyakin bukatar rayuwa.

3972875

 

captcha