IQNA

Kananan yara 77 Ne Suka Yi Shahada A Hare-Haren Isra'ila A Falastinu A Cikin Wannan Shekara

21:13 - November 21, 2021
Lambar Labari: 3486586
Tehran (IQNA) kungiyar kare hakkokin yara ta duniya ta ce, a cikin wannan shekarar da muke ciki Isra'ila ta kashe kananan yara Falastinawa 77.

Jaridar Quds Al-arabi ta bayar da rahoton cewa, kungiyar kare hakkin kananan yara ta duniya ta bayar da rahoton cewa, sojojin Isra'ila sun harbe yara 77 a farkon wannan shekara, 61 a zirin Gaza da kuma 16 a yammacin gabar kogin Jordan da kuma gabashin birnin Kudus.
 
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a ranar yara ta duniya ta ce, tun daga shekara ta 2000 sojojin yahudawan sahyoniya sun kashe kananan yara Palastinawa kusan 2,200.
 
A cewar sanarwar, jami'an tsaron yahudawan sahyoniya na amfani da karfi da gangan a yanayin da bai dace da dokokin kasa da kasa ba, kuma yin amfani da karfi fiye da kima ya zama ruwan dare a wurin  Isra'ila, tare da keta duk wani tsari na kariya wanda dokokin kasa da kasa suka shata.
 
Sanarwar ta ce daga watan Oktoban 2015 zuwa Oktoban 2021, kungiyar ta tattara bayanai da suka hada da hotunan bidiyo na kama kananan yara Falasdinawa 41 tare da tsare su a gidajen kason Isra'ila.
 
Kungiyar ta ce "Isra'ila ita ce gwamnati daya tilo a duniya da ke gurfanar da yara kanana a kotunan soji,  sannan kuma a kowace shekara ana gurfanar da yara Falasdinawa 500 zuwa 700 a kotunan sojin Isra'ila."
 

 

4014852

 

 

 
 
captcha