IQNA

Sanarwar yadda za a gudanar da zaman makokin Tuwayrij a Karbala

20:18 - July 28, 2023
Lambar Labari: 3489552
Karbala (IQNA) Hukumar kula da kula da haramin Sayyidina Abulfadl al-Abbas (a.s) ta sanar da shigowar maziyarta da ke halartar zaman makokin na Tuweerij.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Alam cewa, bisa ga sanarwar da wannan hukuma ta bayar, an yi niyyar shiga kofofi hudu daga cikin kofofi tara da ke cikin haramin Abul Fadl al-Abbas, da sauran kofofi guda biyar an yi nufin sanya su na fita.

Reda Naji Al-Amiri mataimakin darektan hukumar kula da haramin Sayyid Abbas r.a ya ce: An shirya kofofin Haramin ne domin zaman makoki mai suna Tuweerij a ranar Ashura, kuma kamar yadda tsare-tsare suka yi, an bude hudu daga cikin kofofi tara na Harami mai tsarki daga gefen da ke tsakanin wuraren ibadar guda biyu domin shigowar masu zaman makoki, da kuma wasu kofofi guda biyar da aka nufa na fita.

اعلام چگونگی برگزاری عزاداری طُوَیریج در کربلا

A duk shekara a ranakun Tasu'a da Ashura na Hosseini, ana gudanar da zaman makokin shahidan Karbala a wurare masu tsarki da kuma wuraren ibada. Sakamakon kafa kungiyoyin zaman makoki daban-daban, an shimfida jajayen kafet a wuraren ibada a kwanakin da suka gabata da kuma a cikin daren jiya don tunawa da ranar 10 ga watan Muharram.

اعلام چگونگی برگزاری عزاداری طُوَیریج در کربلا

Kungiyoyin makoki da jerin gwano na al'ummar Karbala su ma sun gudanar da shirye-shiryen zaman makoki tun daga ranar farko ga watan Muharram. A bana wasu daga cikin wadannan kungiyoyi sun daga murya domin yin Allah wadai da wulakanta kur’ani mai tsarki da kuma girmama wadannan kur’ani.

 

 

4158539

 

Abubuwan Da Ya Shafa: makoki kur’ani allah girmama muharram
captcha