IQNA

A Yayin Ganawa Da Sheikh Zakzaky Jagora Ya Bayyana Cewa:

Kungiyoyin Gwagwarmayar Falastinawa Na Kan Hanyar Samun Cikakkiyar Nasara

15:31 - October 14, 2023
Lambar Labari: 3489972
Tehran (IQNA) Jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce yunkurin da aka fara a Falasdinu zai ci gaba kuma zai kai ga samun nasara.

Shafin yanar gizo an ofishin jagora ya bayar da rahoton cewa, a yayin da yake ganawa da jagoran Harka Islamiyya a Najeriya Sheikh Ibrahim Zakzakya  yau Asabar a Tehran, Ayatullah Khamenei ya tabo halin da ake ciki a yankunan Falasdinawa, musamamn ma yankin Zirin Gaza da yahudawa suka yi wa kawanya, wanda a halin yanzu yake fuskantar munanan hare-haren wuce gona da iri na Isra'ila, a rana ta bakwai tun bayan harin da kungiyar Hamas ta kai a ranar Asabar din da ta gabata.

Ya ce: “A yau daya daga cikin abubuwan da ke nuna karfin Musulunci shi ne irin abubuwan da suke faruwa a  Falasdinu.”

"Abubuwan da suka faru a 'yan kwanakin nan a Falasdinu, musamman tashin bama-bamai da shahadar mata, yara da tsoffi, suna raunata zuciyar kowane dan Adam mai lamiri, amma kuma suna nuna irin gagarumin karfi na imani da juriya a tattare da al’ummar Falasdinu," in ji shi.

"Kuma da yardar Allah, wannan yunkuri da aka fara a Falastinu zai ci gaba har sai ya kai ga samun nasarar Falasdinawa a kan makiya."

Ayatullah Khamenei ya ce: Wajibi ne kowa a duniyar musulmi ya taimaka wa al'ummar Palastinu.

Jagoran ya ce Lamarin Musulunci yana ci gaba da yaduwa a sassa daban-daban na duniya kamar Afirka, Asiya, Turai da Arewacin Amurka, kuma da yardar Allah zai ci gaba da samun karfi.

Jagoran ya kuma yaba da kokarin Sheikh Zakzaky da na iyalansa, inda ya ce yadda Musulunci ke kara karfi a duniya duk da yawan makirce-makircen da ake kulla masa, hakan ya samo asali ne daga irin wannan kokari da juriya.

 

 

4175192

 

captcha