IQNA

Raya Daren farko na lailatul kadri a kasashen Afrika

16:59 - March 31, 2024
Lambar Labari: 3490899
IQNA - An gudanar da tarukan raya daren lailatul kadari na farko a kasashen Afirka hudu da suka hada da Benin, Chadi, Kenya, da Laberiya, karkashin kulawar bangaren ilimi da al'adu na haramin Abbasi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin sadarwa na yanar gizo na Global Sponsor Network ya bayar da rahoton cewa, an rayar da daren farko na lailatul kadari, wanda ya zo daidai da daren 19 ga watan Ramadan, tare da halartar dimbin mabiya ahlulbaiti da kuma sauran masu son raya wannan dare a kasashen Afirka na Laberiya, Kenya, Benin da Chadi.

An gudanar da wannan biki na ruhin ne tare da hadin gwiwar Cibiyar Nazarin Afirka da ke da alaka da hubbaren Abbasi tare da gabatar da lacca mai taken Falalar Imam Ali (AS) da matsayinsa a Musulunci, irin jajirtattun matsayi na wannan Imami wajen kare Manzon Allah (S.A.W) da bayanin rayuwarsa mai daraja da tsarin rayuwarsa, duk yana daga cikin ayyukan wannan taro.

Haka nan kuma masoya Ahlul-baiti (a.s) sun yi juyayi a cikin wannan dare wanda ya kasance daidai da daren da aka sari Imam Ali (a.s) a masallaci yana ibada.

احیای نخستین شب قدر در کشورهای آفریقایی + عکس

احیای نخستین شب قدر در کشورهای آفریقایی + عکس

احیای نخستین شب قدر در کشورهای آفریقایی + عکس

احیای نخستین شب قدر در کشورهای آفریقایی + عکس

احیای نخستین شب قدر در کشورهای آفریقایی + عکس

 

 

4207856

 

 

captcha