IQNA

Limaman Masallatai A Turai Sun Yi Jerin Gwanon Barranta Daga 'Yan Ta'adda

22:05 - July 09, 2017
Lambar Labari: 3481683
Bangaren kasa da kasa, limaman musulmi a kasashen nahiyar trai sun jerin gwano domin nisanta kansu daga ayyukan 'yan ta'adda masu danganta kansu da addinin muslunci.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Mont Carlo cewa, malaman sun shirya wannan jerin gwanon ne da nufin bayyana wa duniya cewa masu gudanar da ayyukan ta'addanci ba suna wakiltar musulmi ba ne ko addinin musulunci.

Khatib Hassan Al-shalkumi daya ne daga cikin malaman da suka shirya gudanar da wannan babban gangmi a birnin Paris a kasar Faransa ya bayyana cewa, babbar matsalar da ake fuskanta ahalin yanzu ta nuna kyama ga musulmia cikin kasahen turai tana da alaka ne da abubuwan da 'yan ta'adda suke aikatawa da sunan addinin muslunci.

Babbar manufar wannan jerin gwanon ita ce bayyawa mutanen nahiyar turai da duniya baki daya cewa, addinin muslunci addini ne na zaman lafiya ba tashin hankali da ta'addanci ba, kamar yadda 'yan ta'adda suke kokarin nunawa.

A daya bangaren malaman sun yi kira da a dakatar da duk wani aiki na nuna kyama ga musulmi da sunan 'yan ta'adda, domin kuwa musulmi ba su amince da wannan danyen aiki ba, a kan ya kamata su hukumomi su hana duk wani akin kymar musulmi da cutar da su.

3616746


captcha