IQNA

Mai Fafutuka A Bahrain A Takarar Lambar Kare Hakkin Dan Adam Ta Turai

23:58 - August 30, 2018
Lambar Labari: 3482939
Bangaren kasa da kasa, an saka sunan shugaban cibiyar kare hakkin bil adama a Baharain Nabil Rajaba cikin ‘yan takarar lambar kare hakkin bil adama ta kasashen turai.

 

Kamfanin dillanin labaran iqna ya habarta cewa, tashar Lu’ulu’a ta bayar da rahoton cewa, kwamiti na musamman da aka kafa domin fitar da mutane uku da suka taka rawa wajen kare hakkin bil adama a shekara ya saka sunan Nabil Rajab.

Kwamitin ya bayyana cewa, Nabil Rajab ya taka rawar gani maras misiltuwa wajen kare hakkokin bil adama da kuma kare dimukradiyya a Bahrain, wanda sanadiyyar haka tun a cikin shekara ta 2016 ake tsare da shi a gidan kaso.

A kan hakan kwamitin ya ce Nabil Rajab ya cancanci ya zama cikin mutane da za a zaba domin fitarda wanda zai cinye wannan babbar lambar yabo ta kare hakkin dan adam ta nahiyar turai.

Tun a cikin shekara ta 2013 ne aka fara gudanar da wannan shiri na bayar da lambar yabo ta kare hakkin bil adama ta kasashen nahiyar turai, inda a kan zabi mutane da suka taka rawa a wannan fage a duniya domin ba su wannan lambar tare da karramawa.

3742500

 

 

captcha