IQNA

Hoton Bidiyo: Yara ‘Yan Makaranta A Senegal Na Karatun Kur’ani Da Salon Kira’ar Khalil Husari

22:16 - December 16, 2020
Lambar Labari: 3485464
Tehran (IQNA) an nuna wani hoton bidiyo da ke nuna yara a makaranta a kasar Senegal suna karatun kur’ani na bai daya da salon kira’ar Sheikh Mahmud Khalil Husari.

Jaridar yaum Sabi ta bayar da rahoton cewa, a cikin wani faifan bidiyo da ke nuna yara a makaranta a kasar Senegal suna karatun kur’ani na bai daya da salon kira’ar Sheikh Mahmud Khalil Husari dan kasar Masar.

Rahoton ya ci gaba da cewa, duk da shudewar shekaru fiye da arba’in da rasuwar Sheikh Mamhud Khalil Husari, amma ana ci gaba da yin amfani da salon karatunsa na kur’ani mai tsarki a ko’ina  a cikin fadin duniya.

Kasar Senegal tana daga cikin kasashen nahiyar Afirka musamman a  yammacin nahiyar, wadanda suka tasirantu da salon karatun kur’ani mai tsarki irin na makarantar kasar Masar, musannan a bangaren tartil, inda su kan yin koyi da salon karatun wannan babban malamin kur’ani.

A lokutan baya ma an nuna wani faifan bidiyo na wata yarinya ‘yar kasar Indonesia mai suna “Fatemah” wadda take karatun kur’ani mai tsarki salon tilawa na wannan babban malami.

3941514

 

captcha