IQNA

Karatun Kur'ani Daga Fitaccen Makarancin Kasar Pakistan

22:15 - March 27, 2021
Lambar Labari: 3485765
Tehran (IQNA) karatun kur'ani mai tsarki daga fitaccen makaranci dan kasar Pakistan wanda ya yi da salo na musamman.

Abdullah Khaled fitaccen makarancin kur'ani dan kasar Pakistan ya karanta ayoyi daga 96 zuwa 100 a surat Baqarah

Ga tarjamar ayoyin;

96; Kuma lalle ne, za ka same su mafiya kwadayin mutane a kan rayuwa, kuma su ne mafiya kwadayin rayuwa daga wadanda suka yi shirka. dayansu yana son da za a rayar da shi shekara dubu, kuma ba ya zama mai nisantar da shi daga azaba domin an rayar da shi. Kuma Allah, Mai gani ne ga abin da suke aikatawa.
97; Ka ce: Wanda ya kasance makiyi ga Jibirilu, to, lalle ne shi ya saukar da shi a kan zuciyarka da izinin Allah, yana mai gaskatawa ga abin da yake gaba gare shi, kuma da shiriya da bishara ga muminai.
98; Wanda ya kasance makiyi ga Allah da mala´ikunSa da manzanninSa da Jibirila da Mika´ila to, lalle ne, Allah Makiyi ne ga kafirai.
99; Kuma lalle ne hakika Mun saukar, zuwa gare ka, ayoyi bayyanannu, kuma ba wanda yake kafirta da su face fasikai.
100; Shin, kuma a ko da yaushe suka kulla wani alkawari sai wani bangare daga gare su ya yi jifa da shi? a´a, mafi yawansu ba su yin imani.
101; Kuma a lokacin da wani manzo (Muhammadu) daga wurin Allah ya je musu, mai gaskatawa ga abin da yake tare da su, sai wani bangare daga wadanda aka bai wa Littafi, suka yar da Littafin (Alkur´anin) Allah a bayan bayansu, kamar dai su ba su sani ba.

3960353

 

 

 

captcha