IQNA

An Fara Bayar Da Horo Na Hardar Kur’ani A Masallacin Azhar

19:27 - February 09, 2022
Lambar Labari: 3486929
Tehran (IQNA) an fara gudanar da shirin shekara-shekara na horon hardar kur’ani a masallacin Azhar a birnin Alkahira.

Jaridar Yaum Sabi ta bayar da rahoton cewa, a yau ne aka fara gudanar da shirin shekara-shekara na horon harder kur’ani a masallacin Azhar a birnin Alkahira, wanda kuma wannan shi ne karo na hudu da ake gudanar da shiri.

Kwamitin kula da masallacin Al-Azhar ya jaddada wajibcin daukar dukkan matakan kariya domin dakile yaduwar cutar ta Corona, da lura da tazara tsakanin jama’a da kuma shiga dandali da azuzuwan masallacin da abin rufe fuska.

Idan dai ba a manta ba Masallacin Al-Azhar ya koma koyarwa a Darul Al-Karim tun a watan Nuwamban bara, kamar yadda yake tsare a cikin shirin haddar shekara daya da shekara biyu.

Wannan dai ya yi daidai da umarnin Ahmad al-Tayyib Sheikhul-Azhar, dangane da dawo da karatun kur’ani a masallacin Azhar da kuma rassa na kasashen waje.

 

4035128

 

captcha