IQNA

Nadin farar hula musulmi na farko a NYPD

19:30 - February 28, 2023
Lambar Labari: 3488734
Tehran (IQNA) A karon farko an nada wani musulmi farar hula a kwamitin sa ido na 'yan sandan New York.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Aljazeera cewa, Eric Adams magajin garin New York ya nada lauya Mohammad Faridi a matsayin musulmi na farko a kwamitin ‘yan sanda na wannan birni.

“A matsayina na wakilin musulmi na farko a wannan kwamiti, na fahimci cewa al’ummar Musulmi da sauran al’umma marasa rinjaye suna kallona kuma suna son tabbatar da cewa NYPD na yin abin da ya dace,” in ji Faridi bayan nadin nasa. Aikin 'yan sanda na daya daga cikin muhimman abubuwan da NYPD ke yi wa garinmu da kuma kasarmu.

Mohammad Faridi shi ne musulmi na farko kuma farar hula na biyu a cikin kwamitin da ya maye gurbin Stephen Robinson, tsohon Alkalin Alkalan Amurka na gundumar Kudancin New York, wanda zai yi wa'adi na shekaru biyar.

 

4124911

 

captcha