IQNA

Gudanar da tarukan juyayin shahadar Imam Ali (AS) a Karbala

18:44 - April 12, 2023
Lambar Labari: 3488964
Tehran (IQNA) A daren jiya ne aka fara gudanar da zaman makoki da tattaki a ranakun zagayowar ranar shahadar Amirul Muminina Ali (AS) a Karbala.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an gudanar da zaman makoki da tattaki na shahadar Amirul Muminin (AS) a Karbala Ma’ali daga daren jiya 19 ga watan Ramadan.

An gudanar da wannan taro  ne a tsohon yankin Karbala tare da halartar malamai da sauran bangarori na kungiyoyin addini da sauran jama'a.

Wannan taro ya hada da abubuwan da aka saba yi na jawabai da rera baitocin makoki na lokacin da ake tunawa da zagayowar ranar wafatin Imam Ali (A.S.).

Dubun dubatar jama'a daga ciki da wajen kasar Iraki ne suka hallara a Karbala ma'ali a wadannan ranaku domin tarukan lailatul Qadr da kuma ranakun juyayin shahadar Imamin  Ahlul bait na farko.

 

 

 

4133283

 

captcha