IQNA

An kamala taro kwamitin Sulhu na MDD kan zaman lafiya ba tare da wata sanarwa ba

16:00 - April 15, 2024
Lambar Labari: 3490989
IQNA - Guterres ya ce: Zaman lafiya da tsaro na yanki da na duniya suna raunana a kowace sa'a kuma duniya ba za ta iya lamuntar karin yaƙe-yaƙe ba. Muna da alhakin kawo karshen tashin hankalin da ake yi a Yammacin Kogin Jordan, mu kwantar da hankulan al'amura a Labanon, da kuma maido da zirga-zirgar ababen hawa zuwa Tekun Bahar Maliya.

An kamala taro kwamitin Sulhu na MDD kan zaman lafiya ba tare da wata sanarwa ba

Shafin sadarwa na tashar Aljazeera ya bayar da rahoton cewa, kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya fara taronsa na duba halin da ake ciki a yankin yammacin Asiya bayan da Iran ta dauki matakin ramuwar gayya kan gwamnatin sahyoniyawan.

Antonio Guterres, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, ya yi kira da a rage tashin hankali a taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya game da halin da ake ciki a yankin yammacin Asiya.

A farkon taron komitin sulhun, babban magatakardar MDD ya ce: Ana kare wuraren diflomasiyya, kuma Isra'ila ta keta wannan ka'ida ta hanyar kai hari kan karamin ofishin jakadancin Iran da ke Damascus.

Wakilin Amurka a Kwamitin Sulhun: Iran ta yi watsi da wajibcinta na kasa da kasa

Robert Wood, wakilin Amurka a wannan taron, shi ma ya sake nanata zargin da ake yi wa Iran, ya kuma ce wajibi ne komitin sulhu ya bar abin da Iran take yi ba a mayar da martani ba.

Wakilin Koriya ta Kudu a Kwamitin Sulhun: Harin da Iran ta kai jiya ya haifar da damuwa

Wakilin Koriya ta Kudu ya ce a taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya game da martanin da Iran ta mayarwa Isra'ila: "Lokacin da Isra'ila ta kai hari kan ginin Iran, mun yi gargadi."

Wakilin na Japan ya bayyana damuwa game da "sakamakon harin da Iran ta kai wa Isra'ila"; Domin a cewarsa, "yana jefa kowa cikin hadari".

Wakilin Faransa a komitin sulhun ya kuma yi Allah wadai da harin ramuwar gayya da Iran ta kai kan wasu yankunan da ta mamaye.

Wakilin na Birtaniyya ya kuma yi Allah wadai da matakin da Iran ta dauka, ya kuma yi ikirarin cewa wannan matakin na barazana ga rayuwar dubban mutane.

Jakadan kasar Rasha a Majalisar Dinkin Duniya, Vassily Nebenzia, ya ce a lokacin da aka kai hari kan ginin karamin ofishin jakadancin Iran da ke Damascus, mun yi gargadi kan yin Allah wadai da hakan a kwamitin sulhu.

Nebenzia ya ce: Abin da muke gani a yau a kwamitin sulhu shi ne nuna munafunci da ma'auni biyu, kuma wannan abin kunya ne.

Wakilin kasar Sin a komitin sulhun ya kuma bayyana cewa, tsawaita rikicin Gaza zai kara dagula al'amura a yankin.

Gargadin Iran karara: Idan Amurka ta kai mana hari, za mu yi amfani da 'yancinmu na mayar da martani

Karshen taron kwamitin sulhu ba tare da fitar da wata sanarwa ko kudiri ba.

Iran ta kira farmakin ramuwar gayya a kan haramtacciyar kasar Isra'ila da farmakin alkawarin gaskiya.

 

 

4210459

 

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kudiri kwamitin sulhu amfani martani gaza
captcha